<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><hymn_number>182</hymn_number>
<title>Da Cuta da Gajiya A Jeji Can Na Ke LW182</title>
<lyrics>[V1]
 1) Da cuta da gajiya a jeji can na ke,
 Sai Yesu ya same ni, ya rungume ni fa.
 Ya sa ni cikin garkensa da farinciki mai yawa.

[V2]
 KORUS
 Ƙauna ta neme ni, jini ya saye ni,
 Jinƙai marar iyaka ne fa!
 Jinƙan Yesu, ba misalinsa!

[V3]
 2) Miyagun zunubaina ya wanke mini duk.
 Ya kori tsoron raina ya ba ni ƙaunarsa,
 Ya ce da ni ni nasa ne, ba wanda za ya raba mu.
 Korus

[V4]
 3) Azabar da ta samo gafarar laifina,
 Jininsa da ya wanke ƙazantar zuciyata,
 Ina misalin raɗaɗi wanda ya sha saboda ni!
 Korus

[V5]
 4) Yanzu a nan gabansa a cikin haskensa,
 Gun Yesu na ke zaune, Yesu Mai Cetona.
 A ƙare dukan yabonsa? Ko rabi ba na iyawa.
 Korus

[V6]
 5) Gabansa na ke zaune da daɗin rai yanzu.
 Zuwansa na ke jira domin ya kira ni.
 A Sama can in tarbe shi wanda ya zo ya cece ni.
 Korus</lyrics>
</song>